Kotu ta yanke wa tsohon gwamnan Plato Joshua Dariye hukuncin shekaru 14 dazunnan

Kotu ta yanke wa tsohon gwamnan Plato Joshua Dariye hukuncin shekaru 14 dazunnan

- Joshua Dariye yayi mulki a 1999-2007, kotu ta same shi da laifin kwashe kudi

- Ya kwashi biliyoyi daga jiharsa ya kai wasu kasar waje, wasu ya baiwa PDP

- AN shekara takwas ana shariar, kuma kurkuku zai je

Kotu ta yanke wa tsohon gwamnan Plato Joshua Dariye hukunci dazunnan
Kotu ta yanke wa tsohon gwamnan Plato Joshua Dariye hukunci dazunnan

Gwamnan jihar Pilato a zamanin Obasanjo ya kwashi kudi daga jiharsa ya mayar nasa, kuma ya raba wa abokai da ma tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

A hukuncin da aka karkare yau, An same shi da laifukan da suka hada da damfara da kwasar kudin talakawa, da ma fitar da kudaden kasar waje.

Mai shari'a Adebukola Banjoko na babban kotu a babban birnin tarayya, Gudu, Abuja, yana shari'a akan karar tsohon gwamnan jihar filato, Joshua Dariye wanda aka dau sama da shekaru 10 ana yi.

Dariye wanda ya iso harabar kotun da wuri kafin a fara zaman kotun, ya shiga kotun da karfe 9:08am na ranar talata.

Da shiga ta babban riga da aiki baki, da hula baka, Dariye ya zauna a gefen hagu na kotun, ya cire hular, tare da durkusar da kai da kuma addu'a ta wasu sakanni.

Dariye, Sanata ne yanzu dake wakiltar filato ta tsakiya a majalisar wakilai, ana zargin shi da damfarar Naira biliyan 1.162 a lokacin da yake gwamnan jihar filato a 2004.

A yanzu dai, ana jiran ranar da za'a yanke masa ko shekaru nawa zayyi a kulle. Ba'a yi batun ko zai dawo da kudaden ba.

A 2016, Joshua Dariye ya gudu daga PDP ya koma APC ga alama duk don ya tsere wa shari'ar da ake masa wadda a baya an daina ta.

DUBA WANNAN: An dakatar da shariar Dariye saboda zashi bandaki

A 2015 aka maido da shari'ar bayan a baya an wanke shi tsaff da sabulu, cewa ai wai kotun ma batta da hurumin kama shi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel