Tsakanin dan Adam da kuɗi: Gaskiya ban ji daɗin Naira 2,000 da aka bani ladan tsuntuwar 500,000 ba - Inji wani matashi

Tsakanin dan Adam da kuɗi: Gaskiya ban ji daɗin Naira 2,000 da aka bani ladan tsuntuwar 500,000 ba - Inji wani matashi

- Aikin lada da zobe shi duk a lokaci daya

- Wani saurayi yayi korafin ladan tsuntuwar da wani mutum ya ba shi bayan mantuwar kudi da yayi masu yawa a shagonsa

Wani ɗan Najeriya mai suna Ifeanyi da ya tsinci kuɗin wani mutum da yayi siyayya a shagonsa har Naira 500,000 ya bayyana rashin jin daɗinsa ƙarara game da yadda mai kuɗin ya ba shi Naira dubu biyu kacal.

Tsakanin dan Adam da kuɗi: Gaskiya ban ji daɗin Naira 2,000 da aka bani ladan tsuntuwar 500,000 ba - Inji wani matashi
Tsakanin dan Adam da kuɗi: Gaskiya ban ji daɗin Naira 2,000 da aka bani ladan tsuntuwar 500,000 ba - Inji wani matashi

Ifeanyi dai ya wallafa a shafin sadarwarsa na Twitter domin bayyana irin abinda ya kira kwauro, a cewarsa duba da yawan kuɗin da kuma cewar shi mai kuɗin ya manta inda ya ajiye su, kamata yayi a ce ya ba shi abinda yafi haka.

Ya bayyana cewa, a lokacin da mutumin ya dawo yana cigiyar ko ya bar kuɗin a shagonsa, sai na ɗagn tsokane shi na ce masa ban gani ba, kawai sai na ga ya juya zai tafi, daga nan ne na kira shi na miƙa masa kuɗinsa.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun kwanaki 2 don bikin karamar sallah

Sai da ya rungume ni don tsananin murna, amma wai ga mamaki na sai naga ya ba ni dubu biyu kacal.

Wannan jawabin da Ifeanyi yayi a shafin nasa na Twitter ya sanya mutane mayar masa da martani, inda wasu suke cewa da ma ba don Allah ya bayar ba wasu kuma suke cewa tunda ba nasa ba ne ai bai kamata ya damu ba.

Tsakanin dan Adam da kuɗi: Gaskiya ban ji daɗin Naira 2,000 da aka bani ladan tsuntuwar 500,000 ba - Inji wani matashi
Tsakanin dan Adam da kuɗi: Gaskiya ban ji daɗin Naira 2,000 da aka bani ladan tsuntuwar 500,000 ba - Inji wani matashi

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng