12 ga watan Yuni: Ya zama dole IBB ya ba yan Najeriya hakuri - Adeoti

12 ga watan Yuni: Ya zama dole IBB ya ba yan Najeriya hakuri - Adeoti

Wani dan takarar gwamna a karkashin inuwar All Progressives Congress (APC) a zaben jihar Osun da zaa yi a ranr 22 ga watan Satumba, Alhaji Moshood Olalekan Adeoti ya shawarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja, janar Ibrahim Babangida da ya ba yan Najeriya hakuri akan juyin mulkin 12 ga watan Yunin 1993.

Adeoti wanda ya kasance sakataren gwamnatin jihar Osun ya yabama shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Damokradiyya da yayi tare kuma da karrama marigayi Moshood Abiola (MKO).

A sakon ranar Damokradiyya das a hannun kakakin kungiyar yakin zaben Moshood Adeoti, Mista Kayode Agbaje, Adeoti yace lallai ya zama dole IBB ya bada hakuri kan rawar da ya taka wajen juyin mulki a zaben da kowa ya san Abiola ne yayi nasara.

12 ga watan Yuni: Ya zama dole IBB ya ba yan Najeriya hakuri - Adeoti
12 ga watan Yuni: Ya zama dole IBB ya ba yan Najeriya hakuri - Adeoti

Adeoti yace yan Najeriya sun cancanci ban hakuri daga Babangida kan satar da yayi da tsakar rana.

Ya bukaci tsohon shugaban kasar da ya tattara karfin gwiwa sannan ya ajiye abunda abokansa ka iya fadi ya ba yan Najeriya hakuri domin ya samu kwanciyar hankali.

KU KARANTA KUMA: Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote

Ya kuma shawarci gwamnati da ta karrama shi ta hanyar sanyawa muhimman abubuwa sunansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng