Shugaban Koriya ta Arewa ya tafi Singapore da ban daki tafi da gidanka
Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya je Kasar Singapore domin ganawa da takwaransa na Amurka Donald Trump.
Daga cikin matakan tsaro da Kim ya dauka har da na tafiya da bandakin tafi da gidanka saboda gujewa yan leken asiri a kashinsa.
Rahotanni sun kawo cewa, Daraktan tsaro na Koriya ta Arewa ya tafi Singapore da jiragen sama biyu inda ya dauki bandaki sukutun domin amfanin shugaban kasar su.
Sannan kuma Kim ya tafi da duk wani kayan abinci da zai ci a yayin ganawar su da Trump wanda ke kunshe da dumbin tarihi.
Bisa ga rahoto, ya tafi da masan sa domin gujewa yunkurin yan leken asiri da za su iya nazari akan kashi da fitsarinsa domin gano rayuwarsa ta sirri.
KU KARANTA KUMA: Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki
Koriya ta Arewa dai ta dauki tsauraran matakan tsaro a yayin da shugabanta ke gana wa da Trump a Singapore.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng