Wani mutum ya gamu da ajalinsa a yayin gujewa jami'an yan sanda

Wani mutum ya gamu da ajalinsa a yayin gujewa jami'an yan sanda

- Garin gudun ceton rai ya kai ga ya hallaka kansa

- Ya firgita ne bayan da 'yan sanda sun kawo sumeme yankin nasu

- Su kuma suna tsaka da yin karta, sai suka zata su aka zo kamawa

Wani mutum mai suna Oge ya gamu da ajalinsa a yayin da yake gujewa yan sanda, sakamakon nitsewa da yayi a ruwan Elechi dake unguwar Diobu a Garin Fatakwal.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa a yayin gujewa jami'an yan sanda
Wani mutum ya gamu da ajalinsa a yayin gujewa jami'an yan sanda

Rahoton da ya iske mu na cewa, mamacin suna zaune da abokansa ne da misalin karfe 4:00pm na yamma suna wasan karta a yayin da yan sanda suka kutso kai tare da fara harbi a iska, nan take kowa ya arta ana kare domin tsira.

Wani mazaunin yankin ya shaida mana cewa Oge ya gudu ne domin gujewa kamun ƴan sandan, amma sai ya fada ruwan kuma aka yi rashin sa'a bai iya ruwa ba.

Bayan rasuwar Oge a cikin wannan ruwa ne sai wasu matasa dake yankin suka fara zanga-zangar adawa da jami'an ƴan sanda da kuma nuna rashin jin dadin yadda jami'an tsaron ke wulakanta ƴan Adam.

Matasan dun dauki gawar mamacin zuwa wani asibiti dake kusa da yankin idan a nan aka tabbatar musu da cewa ya rasu, nan take suka dauki gawar zuwa caji-ofis ɗin yan sandan domin nuna rashin jin daɗin su.

KU KARANTA: Wani ɗalibi ya ɗebo ruwan dafa kansa, bayan satar wayar salula da kuma Kwamfuta

Wani wanda ya ganewa idonsa yadda lamarin ya faru mai suna Kelvin ya shaidawa manema labarai cewa "Oge ya fita da gudu ne cikin firgici don ya gujewa yan sandan sai aka yi rashin sa'a ya fada ruwa kuma gashi bai iya ba".

"Ƴan sandan haka suka tsaya suna kallonsa yana ta ihun neman taimako su kuma mutane sun kasa yin wani abu domin gudun kar ƴan sandan su kama duk wani wanda yayi yunƙurin cetonsa".

Kakakin hukumar ƴan sanda na Fatakwal Mr. Nnamdi Omoni ya ce jami'an ƴan sandan ba abinda ya haɗa su da kowa face sun je yankin ne domin kai sumame ga wasu ƴan-fashi da makami.

Ya ce "Ƴan sandan suna bakin aikinsu ne wajen neman wasu yan fashi da makami, ba shi suke nema ba shi kuma ya tsorata cikin firgici ya faɗa ruwa, ko jikinsa kuka duba zaku ga babu harbi ko daya balle ace ƴan sanda ne suka yi sanadin mutuwarsa".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng