Wulakanta Al-Kur’ani kafirci ne – Dr. Bashir Aliyu Umar
Babban malamin nan na addinin Musulunci kuma limamin masallacin Alfurkan dake Kano, Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar ya ja hankulan musulmai kan yadda wasu ke sakaci da littafi mai tsarki.
Ya yi gargadi kan a guji wulakanta Kur’ani ta hanyar ajiye shi a kasa, yadda zai bayu zuwa ga wasu su taka shi ba tare da sun sani ba, musamman a wannan lokacin da al’umma da dama suke yin Ibadar I’itikafi a masallatai.
Malamin yayi wannan kira ne a yayin da yake gudanar da Tafsirin Al-kurani mai girma na watan Ramadana kamar yadda aka saba duk shekara.
Wannan jan hankali ya biyo bayan yawan korafi da ake samu kan yadda wasu ke yiwa littafi mai tsarki rikon sakainar kashi suna ajiye wa a kasa, wanda hakan yake sanya wasu su taka shi ba tare da sun sani ba.
KU KARANTA KUMA: 2019: Talakawa ne zasu yanke hukunci kan wanda zai zamo shugaban kasar Najeriya na gaba - Keyamo
Malamin ya jaddada cewa duk mutumin da ya wulakanta Al-Kurani toh babu shakka ya kafirta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng