2019: Kamfunna 400 ne zasu fara aikin tsarkake Neja Delta daga danyen mai da aka shekara 40 ana gurbaata yankin dashi

2019: Kamfunna 400 ne zasu fara aikin tsarkake Neja Delta daga danyen mai da aka shekara 40 ana gurbaata yankin dashi

- Shekaru sittin ana tatsar mai daga yankin Neja Delta

- Masu kokarin a gyara muhallin sun rasa ransu a baya karkashin Sani Abacha

- A yanzu gwamnatin APC ta sami yadda zata yi don kawo zaman lafiya

Kmfunna 400 ne zasu fara aikin tsarkake Neja Delta daga danyen mai da aka shekara 40 ana gurbaata yankin dashi
Kmfunna 400 ne zasu fara aikin tsarkake Neja Delta daga danyen mai da aka shekara 40 ana gurbaata yankin dashi

A ranar litinin ne gwamnatin tarayya tace kusan kamfanoni 400 na gida da waje suka saftace Ogoni wanda ya gurbace da mai.

Karamin ministan muhalli, Ibrahim Jibrin ya bayyana haka a Nnimmo Bassey National Colloquium a Abuja yace za a tura yan kwangila filin nan da watan Augusta ko Satumba na wannan shekarar.

Ministan ya Kwatanta Nnimmo Bassey da masoyin muhalli, daya daga cikin masu tsaftace Ogoni wanda yayi bikin cika shekaru 60 a matsayin dan kasa na nagari, yace gwamnatin ta kirkiro wata hanya ta tsaftace Ogoni wanda zai kai har watan Disamba na 2019.

Filin Ogoni, wanda ya gurbace da mai ya kawo asarar rayukan tudu da na cikin ruwa, amma Gwamnatin mai ci yanzu ta dau alkawarin tsaftace filin.

Yace, mun samu tsari da lokacin da zai kaimu zuwa watan Disamba na 2019. An dade ana karya alkawari, wanda yasa mutane suka zargi muma bazamu cika ba a lokacin da mukayi namu alkawarin.

DUBA WANNAN: Wata yarinya tayi kokarin kashe kanta a gadar sama ta Legas

"Mu na bin tsarin yanda yakamata kuma munsa kamfanoni 400,mun fitar da tsarin bangarori 14 cikin 26 kuma yanzu muna duba nawa zasu ci.

"Muna son fara aikin nan da watan Augusta ko Satumba da izinin Ubangiji."

Yace wakilan majalisar dinkin duniya sun iso Najeriya a juma'a da ta gabata kuma kashi 18 cikin dari na tataunawar su akan Ogoni ne.

Bassey wanda Architect ne kuma shugaba ne a kungiyar taimakon kai da kai mai suna co-founded Environmental Rights Action, ERA ya maida hankali akan jakadancin hakkokin muhallli a 1993.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel