Kashe kai: Hukumomi na kokarin ciro gawar ko ceto wata mata da ta fada ruwa daga gadar Legas
- Mutane kan gaji da rayuwa suce zasu kashe kansu
- A jihar Legas kisan kai yakan kai mutane babbar gada mai nisa idan an fado
- Ana tsammanin wata yarinya ta kashe kanta ne a jiya
Jami'an hukumar taimakon gaggawa ta jihar Legas ta fara neman wata budurwar da ake zargin ta fada cikin ruwan Legas daga gada ta uku ta cikin gari a yammacin ranar lahadi.
Wani bidiyo yana ta yaduwa na wata budurwar da ta aje kayayyakin motsa jikin ta a gadar kafin ta fada ruwan.
Har yanzu dai majiyarmu bata tabbatar da ingancin labarin ba.
Amma wani jami'in taimakon gaggawa ya sanar da wakilinmu cewa jami'ai suna gurin da aka ce abun ya faru amma basu samu komai ba.
DUBA WANNAN: Barawon ma'aikacin banki yazo hannu
Da muka tuntubi Adesina Tiamiyu, shugaban hukumar taimakon gaggawar, yace cibiyar tasu tana dai neman budurwar.
"Labari ne da muka samu amma muna kokarin tattara shaidu" Mista Tiamiyu yace
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng