An gano wani ama'aikacin banki dake dauki dai-dai har N3m daga ajiyar mutane
- Hukumar bankin ta yi qarar asusun da aka maida kudin inda daga baya aka kulle shi
- Mamallakan asusun bankin da aka rufe, wadanda basu san ana amfani da asusun nasu gurin damfarar ba, sun kai kansu rassan bankunan domin korafi
- Hukumar bankin sun mika su ga yan sanda
Hukumar yan'sanda ta jihar Legas ta na neman wani ma'aikacin banki da aka sani da Bunmi sakamakon zargin shi da ake da damfarar wasu kwastomomin banki.
Majiyarmu ta gano cewa Bunmi ya shiga asusun bankin kwastomomi inda ya waskar da sama da miliyan 3 zuwa wasu asusun nashi.
Wakilinmu ya gano cewa : an gano damfarar ne bayan da mamallakin asusun yayi koke game da layar zaka da kudaden shi suka yi, wanda ya fargar da bankin.
Mai magana da yawun hukumar yan'sandan yanki na 2 ,CSP Dolapo Badmos, tace ana cigaba da bincike inda aka yi sa'ar kama masu taimakawa Bunmi - Babalola Akinyele, wanda aka fi sani da Olumba ; da Adeshina Adenekan, wanda aka fi sani da Oluwo Ake.
Tace mutanen biyu sunyi dabara ga mamallakan asusun inda suka samu lambar asusun, sai suka turawa wanda ake zargin.
Badmos tace Naira miliyan 3 aka gano yanzu.
"Tsakanin nuwamba 2017 da janairu 2018,mun kama mutane biyu wadanda suka Kware gurin shiga asusun bankin mutane.
Daya daga cikin su, Babalola Akinyele, yana aiki da wani Bunmi, ma'aikacin bankin Zenith.
DUBA WANNAN: Kungiyar Musulmi sun fasa daukar mataki kan FALZ
Aikin Bunmi shine shiga asusun kwastomomi da waskar da kudin su zuwa wani asusun na daban wanda Adeshina Adenekan ya kawo, wanda daga baya yake cire kudin da katin banki na daban inda daga baya yake kawowa abokan damfarar shi nasu kason.
Akinyele da Adenekan suna karbar kashi goma goma cikin dari, inda Bunmi ke mallake sauran. Suna cire kudin da katin bankine gudun kada su shiga bankin a kamasu. A yanzu dai Naira miliyan 3 aka gano."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng