Tashin hankali: Wani mutum ya fita daga cikin motar sa ta alfarma ya yi allan-baku cikin teku a Legas

Tashin hankali: Wani mutum ya fita daga cikin motar sa ta alfarma ya yi allan-baku cikin teku a Legas

- Hukumomi a jihar Legas na kokarin gano mamallakin wata motar alfarma da ya bar ta a tsakiyar titi sannan ya yi allan-baku cikin tekun kasan gadar Third Mainland

- Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Legas (LASEMA) na kokarin binciko dalilin da ya saka mutumin aikata hakan

- LASEMA ta ce tana kokarin tabbatar da maganganun da shaidun gani da ido suka fada masu dangane da fadawar mutumin cikin tekun

Hukumomi a jihar Legas na kokarin gano mamallakin wata motar alfarma da ya bar ta a tsakiyar titi sannan ya yi allan-baku cikin tekun kasan gadar Third Mainland.

Ya bar motar ta sa kirar Ford Explorer ta miliyoyi dake da lambar mallaka APP 190CE a saman gadar da ba ya rabuwa da gudanarwar ababen hawa.

Tashin hankali: Wani mutum ya fita daga cikin motar sa ta alfarma ya yi allan-baku cikin teku a Legas
Gadar Third Mainland a Legas

Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Legas (LASEMA) na kokarin binciko dalilin da ya saka mutumin aikata hakan duk da sun yi amanna cewar ya kasha kan sa ne.

DUBA WANNAN: Duba hotunan tarbar ban girma da Buhari ya samu a kasar Moroko

LASEMA ta ce tana kokarin tabbatar da maganganun da shaidun gani da ido suka fada masu dangane da fadawar mutumin cikin tekun.

An sha samun afkuwar irin wannan matsala ta zundumawa cikin teku a jihar Legas, domin ko a shekarar da ta gabata saida fadawar wani likita cikin tekun ta jawo cece-kuce da musayar mabanbantan ra’ayi a tsakanin mutanen Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng