Yanzu-yanzu: An yi yarjejeniyar gina layin dogon bututun mai daga Najeriya zuwa kasar Maroko
Shugaban Muhammadu Buhari da sarkin Maroko, Mai martaba Muhammad na shida sun kaddamar da tattaunawa da yarjejeniya na karfara tattalin arzikin kasashen biyu.
Shugabannin kasashen biyu sun shaida rattaba hannun kasashen biyu a yarjejeniyar gina layin dogon bututun albarkatun mai fetur daga Najeriya zuwa kasashen Afrika ta yamma da kuma kasar Maroko.
Wadanda suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya sune Manaja a kamfanin NNPC, Mr Farouq da kuma ministan man Maroko, Mrs Amina Benkhadra.
KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sauka kasar Moroko, an masa tarbar girma
Kana shugaba Muhammadu Buhari da sarki Muhammad VI sun shaida yarjejeniyar gina babban masana’antar hada sinadarin takin zamani wato Ammonia, wanda shugaban sanya hannun jarin Najeriya, Mr Uche Orji da Mr Mostafa Terrab na Maroko suka rattaba hannu.
Bugu da kari, shugabannin kasashen biyu sun shaida rattaba hannu kan takardan yarjejeniya tsakanin ma’aikatar aikin noman Najeriya da kuma na kasar Maroko wajen shirya horo ga manoma da ma’aikata wanda ministan aikin noman Najeriya, Cif Audu Ogbeh da ministan noman Maroko, Mr Aziz Akhannouch suka rattaba hannu.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Rabat na kasar Morocco bayan ya bar Najeriya ranar Lahadi, 10 ga watan Yuni.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng