Yanzu-Yanzu: Bam ya tashi da yara 'yan kanana 3 a garin Mubi

Yanzu-Yanzu: Bam ya tashi da yara 'yan kanana 3 a garin Mubi

Labarin da muke samu yanzu yanzu da dumin sa na nuni ne da cewa wani bom din da wasu yara kanana su uku suka tsinta da yammacin yau ya tashi da su a garin Mubi da ke cikin jihar Adamawa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Mun samu dai cewa yanzu haka daya daga cikin yaran ya mutu nan take sannan kuma sauran biyu suka samu mummunan raunuka kuma suna karbar kulawa daga jami'an lafiya.

Yanzu-Yanzu: Bam ya tashi da yara 'yan kanana 3 a garin Mubi
Yanzu-Yanzu: Bam ya tashi da yara 'yan kanana 3 a garin Mubi

KU KARANTA: Bakin kishi ya sa wani saurayi yi wa budurwar sa yankan rago

Legit.ng dai ta samu cewa lamarin ya faru ne a yau Lahadi a wani wurin da ake kira Filin Ajakuta inda ake tara karafa zuwa kudancin Najeriya.

Tuni dai kwamishin watsa labarai kuma kakakin gwamnatin jihar ta Adamawa Ahmad Sajo wanda ya tabbatar wa da majiyar mu ta BBC da faruwar lamarin.

A wani labarin kuma, datun da ke iske mu na dauke ne da labarin wani matashi a garin Potiskum mai suna Muhammad Isa Adamu da tsananin kishi ya sanya ya hau dokin zuciyar sa ya yi wa budurwar sa mai suna Hauwa yankan rago.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyoyin mu, matashin ya bayyana cewa ya aikata wannan danyen aikin ne saboda iyayen budurwar sun ki amincewa ya zama mijin ta shi kuma ba wadda yake so kamar ta a duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng