Abubuwa 5 da Obasajo ya fadi a sabuwar wasikarsa ga Buhari

Abubuwa 5 da Obasajo ya fadi a sabuwar wasikarsa ga Buhari

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya saki sabuwar wasikar ranan Juma’a, watanni 5 bayan sakin na farki inda yace Buhari ya gaza.

A wani jawabin da mai magana da yawunsa, Kehinde Akinyemi, ya saki, Obasanjo y ace gwamnatin Buhari na shirin kulla masa sharri.

Yace ya samu labari daga majiya mai karfi cewa an sanya sunansa cikin wadanda gwamnatin tarayya ke shirya yiwa bita da kulli.

Karanta abubuwa 5 da ya ce:

1.Buhari na shirin kulleni a kurkuku

Obasanjo ya ce kaidin da gwamnati ke shirya masa na kwace katin fita kasar wajnesa da kuma garkame shi

2.Saraki da Dogara na fuskantan kalubale

Obasanjo ya ce shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki,da kakakin majalisa, Yakubu Dogara, na fuskantan kalubale game da wannan gwamnati.

KU KARANTA: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

3.Yan Najeriya na rayuwa cikin tsoro

Tsohon shugaban kasa ya ce yan Najeriya na cikin tsoro gabanin zaben 2019 saboda shirin sake takara da shugaba Muhammadu Buhari ke yi.

4.Buhari na danne yan adawa

Obasanjo ya tuhumci shugaba Buhari da yin amfani da duk wani kafa domin danne yan adawa.

5. Shirye nike da fuskantar bincike amma akan ka’ida daya

Tsohon shugaban kasan ya ce shirye yake da fuskantar bincike kan zargin babakeren kudin wutan lantarki $16 billion amma gaban masu tsoron Allah kuma masu zaman kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng