'Yan Shi'a sun yi bikin tunawa da ranar Qudus

'Yan Shi'a sun yi bikin tunawa da ranar Qudus

Zirga - zirga ta tsaya cak jiya a cikin birnin Kaduna sakamakon tattakin da mabiya aqidar shi'a suka yi don tunawa da ranar Qudus ta duniya

'Yan Shi'a sun yi bikin tunawa da ranar Qudus
'Yan Shi'a sun yi bikin tunawa da ranar Qudus

Zirga - zirga ta tsaya cak jiya a cikin birnin Kaduna sakamakon tattakin da mabiya aqidar shi'a suka yi don tunawa da ranar Qudus ta duniya.

Sunyi tattakin ne cikin lumana a titin Ahmadu Bello, inda suka nuna bukatar su ta gwamnati ta sakar musu shugaban su Sheikh Ibrahim Zakzaky, sannan kuma sun nuna rashin jin dadin su da irin zaluncin da al'ummar kasar Palestine suke fuskanta a hannun kasar Isra'ila.

DUBA WANNAN: Daliban wata jami'a sun rubuta jarrabawa akan Ramos da Salah

A jawabin da shugaban su na Kaduna yayi, Sheikh Aliyu Tirmizi, yace taken zanga zangar lumanar su shi ne: "A saki Sheikh Zakzaky "

Sheikh din ya kushe abubuwan da ke faruwa a kasar Palestine, harda dawo da masallacin Al-Aqsa birnin Qudus da kuma cigaba da kashe Falasdinawa da kasar Isra'ila take yi.

Malamin yace kungiyar zata cigaba da gabatar da zanga - zangar cikin kwanciyar hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng