Labari mai dadi: Duban irin gudumawar da Turkiyya ta aikowa da marayun Najeriya

Labari mai dadi: Duban irin gudumawar da Turkiyya ta aikowa da marayun Najeriya

Wata kungiyar bayar da tallafi ga marasa karfi ta kasar Turkiyya ta aikowa da wasu marayu dake babban birnin tarayya kayan sallah

Labari mai dadi: Duban irin gudumawar da Turkiyya ta aikowa da marayun Najeriya
Labari mai dadi: Duban irin gudumawar da Turkiyya ta aikowa da marayun Najeriya

Wata kungiyar bayar da tallafi ga marasa karfi ta kasar Turkiyya ta aikowa da wasu marayu dake babban birnin tarayya kayan sallah. Shugaban kungiyar mai suna Darul Arkam, Yunus EMre Akyol shine ya sanar da hakan ga manema labarai, inda yake cewa, sun raba kayan sallah ga marayu guda 70 dake birnin Abuja.

DUBA WANNAN: Daliban wata jami'a sun rubuta jarrabawa akan Ramos da Salah

Akyol ya bayyana cewa, kasar Turkiyya ce ta aiko da kayan, inda ita kuma kungiyar su ta Darul Arkam ta rabawa marayu kayan.

Ya ce, bayan wannan kuma sun sake rabawa iyalai marasa karfi 200 kayan abinci, sannan kuma sun ciyar da mutane 1000 buda baki duk a cikin wannan wata mai alfarma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel