Wani dutse mai aman wuta ya fashe yayi sanadiyyar mutuwar mutane 109

Wani dutse mai aman wuta ya fashe yayi sanadiyyar mutuwar mutane 109

An tabbatar da cewa mutanen da suka rasa rayukan su a sanadiyyar fashewar dutse nan na Feugo mai aman wuta a yankin Guatemala sun karu inda suka kai kimanin 109

Wani dutse mai aman wuta ya fashe yayi sanadiyyar mutuwar mutane 109
Wani dutse mai aman wuta ya fashe yayi sanadiyyar mutuwar mutane 109

An tabbatar da cewa mutanen da suka rasa rayukan su a sanadiyyar fashewar dutse nan na Feugo mai aman wuta a yankin Guatemala sun karu inda suka kai kimanin 109. Hukumomin Guatemala sun sanar da cewar an kuma gano wasu gawarwaki guda 10 saboda haka wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar fashewar dutsen sun kai su 109.

DUBA WANNAN: Daliban wata jami'a sun rubuta jarrabawa akan Ramos da Salah

Hukumomin sun kuma bayyana cewa fiye da mutane 200 ne suka bata, inda a yanzu haka ake ta faman neman su ruwa a jallo.

Wata hukumar bada agajin gaggawa ta sanar da cewa sanadiyyar tsananin zafi da ya karu a yankin Harap inda dutsen Fuegon ya fashe, hakan ya tilasta ma'aikatan da suke neman wadanda suka batan dakatar da ayyukan su.

Rahotanni sun nuna cewa hukumomin yankin sun lura da cewar dutsen zai iya fashewa a ranar Lahadin data gabata amma kuma basu dauki wani mataki na fitar da al'ummar wuraren daga yankin ba.

Ana dai hasashen cewa kimanin mutane miliyan 1.7 ne suka kalubalantu ta sanadiyyar fashewar dutsen a Guatemala.

An ce dai idan kana duniya kallo bai kare maka ba, akwai duwatsu kala-kala a duniya kuma wannan ba shine karo na farko da dutse ya fara fashewa ko yayi ambaliyar wuta ba a duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng