Tsintsiya madaurinki daya: An gano Dolapo Osinbajo tana taya Aisha Buhari daurin dankwali
Aminci na gaskiya ba wai sai ka tallafawa mutum da kalamai ko wani kyakyale ba, tallafawa mutane da karfinka a lokacin da bukatar yin hakan ta taso shine ya fi.
Uwargidan shugaban kasa da ta mataimakin shugaban kasa sun nuna misali ga abunda ake nufi da tallafawa juna musamman a tsakanin mata.
A wani hoto da Bashir Ahmad, hadiin shugaban kasa ya wallafa a shafinsa, an gano Dolapo Osinbajo tana daurawa Aisha Buhari dankwalinta.
Kalli hoton a kasa:
A baya Legit.ng ta rahoto cewa uwargidan shugaban kasa ta nuna yabawa da tarin godiya ga mutanen da suka hallarci daurin auren kaninta.
KU KARANTA KUMA: Kasuwa ta bude mun tunda Buhari ya kaddamar da June 12 – Mai siyar da jarida
Aisha ta wallafa a shafinta na twitter cewa ta ji dadin yadda aka kammala bikin dan uwan nata cikin aminci da nasara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng