Mazan jiya: A yau marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekaru 20 da mutuwa
Tafiya tayi nisa Allah ya ji kan mazan jiya. A yau ne marigayi ntsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Sani Abacha ya cika shekaru asirin da rasuwa.
An dai haifi janar Sani Abacha ne a ranar 20 ga watan Satumba ta shekarar 1943 a cikin birnin Kano.
Ya yi karatunsa na Firamari a City Senior Primary School, Kano, sai ya tafi Government College, Kano, 1957-1962, Kwalejin horas da sojoji ta Kaduna Najeriya, 1962-1963.
Daga nan sai ya tafi kwalejin Horrs da Sojoji ta Aldershot dake kasar Ingila, 1963, Kwalejin horar da dakaru soji ta Warminster, ta Birtaniya 1966, 1971 Kwalejin sojoji ta Jaji dake Kaduna, 1976, Kwalejin nazarin manufofi da tsara dabarun mulki ta Kuru, Jos, 1981.
Tun daga juyin mulki na farko a Najeriya a shekarar 1966 janar Sani Abacha ke taka rawar gani a kasar.
KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki bata yi barazanar tsige shugaban kasa ba – Ministan Buhari
Allah ya amshi ran Abacha a ranar 8 ga watan Yuni shekarar 1998 yana da shekaru 54 a duniya.
Ya rasu ya bar matar aure daya Hajiya Maryam Abacha da 'ya 'ya tara mata uku da maza shida.
A halin da ake cikin, Legit.ng ta rahoto a bayan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar demokradiyyar Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yni, tare da karrama marigayi Abiola a matsayin tsohon shugaban kasa.
Sai dai majalisar dattawa tayi adawa da hakan inda tace har yanzu ranar 29 ga watan Mayu itace ranar rantsar da sabbin shugabanni na kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng