Duniya ina zaki damu: An kama wasu daliban sakandare sun hada kungiyar asiri, da kuma laifin sace - sace

Duniya ina zaki damu: An kama wasu daliban sakandare sun hada kungiyar asiri, da kuma laifin sace - sace

A ranar Alhamis dinnan ne hukumar 'yan sandan jihar Ondo ta kama wasu dalibai biyu na makarantar sakandare tare da wasu mutane 8 da laifin hada kungiyar asiri da kuma satar ababen hawa a yankunan su

Duniya ina zaki damu: An kama wasu daliban sakandare sun hada kungiyar asiri, da kuma laifin sace - sace
Duniya ina zaki damu: An kama wasu daliban sakandare sun hada kungiyar asiri, da kuma laifin sace - sace

A ranar Alhamis dinnan ne hukumar 'yan sandan jihar Ondo ta kama wasu dalibai biyu na makarantar sakandare tare da wasu mutane 8 da laifin hada kungiyar asiri da kuma satar ababen hawa a yankunan su.

Daliban biyu, yan makarantar Oroke High school, dake garin Akugba Akoko, kamar yanda yan sandan suka fada, an kama su ne bayan samun labari da akayi cewa zasu tada hatsaniya a jami'ar garin.

DUBA WANNAN: Dubi irin cigaban da ma'aikatar Sufuri zata kawowa matasan Najeriya

Kwamishinan yan sandan jihar Ondo, Mista Gbenga Adeyanju, wanda ya samu zantawa da manema labarai a lokacin da aka kama masu laifin, yace yan ta'adda basu da gurin zama a jihar.

Biyu daga cikin wadanda aka kama, dalibai ne a jami'ar Adekunle Ajasin, Akugba Akoko (AAUA)

Adeyanju yace wadanda ake zargin sun bayyana cewa sune yan kungiyar asirin 'Aiye and Scorpions' kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar dasu a gaban shari'a.

Kwamishinan yace an kama mutane biyar da ake zargi da satar ababen hawa sakamakon satar motoci masu kirar 'Nissan Primera da Toyota Bus' wadanda mallakin wata makaranta ce a jihar Legas.

Adeyanju yace wani mai suna Oluwaseun Mayowa mai shekaru 41, ya bayyana cewa ya hada kai da wasu mutane 3, sun sace sannan kuma suka sayar da motar tasi mallakin dan uwanshi.

Kamar yanda kwamishinan yace, Mayowa da farko yace barayin sun daure mishi hannaye da kafafu, inda suka gudu da mota kirar Nissan Almera mai lamba AKR 898 XA. Yace an kwace motar ne a babbar hanyar Igbara Oke da Owena Owode.

Amma bayan an tsananta bincike, ya bayyana sunayen wadanda suka taimaka mishi da, Niyi Akintoye, mai shekaru 42 da kuma Tunde John, mai shekaru 40, duk daga Akure babban birnin jihar.

Yace akwai Olaoke Paul a lokoja wanda ya matsa sai an siyar da motar akan naira 150,000.

"A yanzu dai an samo motar kuma za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a kotu." inji Adeyanju

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng