Mashahurin mai kudin Najeriya ya ba Buhari kyautar motocin alfarma 2

Mashahurin mai kudin Najeriya ya ba Buhari kyautar motocin alfarma 2

Fitaccen mai kudin nan dan Najeriya kuma shugaban kamfanin da ke kera motoci a Najeriya na IVM Innoson watau Cif Innocent Chukwuma a ranar alhamis din da ta gabata ya ba wata kungiyar kamfe din Buhari na zaben 2019 kyautar motoci biyu.

Motocin dai wadanda dukkan su sabbi ne samfurin SUV IVM G5 da kuma bas din Innoson samfurin IVM 5000A an mika su ne ga kungiyar Muhammadu Buhari/ Osinbajo (MBO) Dynamic Support Group da ke fafutukar ganin shugaba Buhari ya zarce a 2019.

Mashahurin mai kudin Najeriya ya ba Buhari kyautar motocin alfarma 2
Mashahurin mai kudin Najeriya ya ba Buhari kyautar motocin alfarma 2

KU KARANTA: Buhari yayi nasara a kotu

Legit.ng ta samu cewa fitaccen mai kudin dai ya bayyana kyautar motocin a matsayin wata gudummuwar sa ga shugaban kasar.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu daga majiya mai tushe ta tabbatar mana da cewa shugabannin majalisaun tarayyar Najeriya sun sanar da rufe majalisun da suka hada da majalisar dattijai da ta wakilai har sai zuwa ranar 3 ga watan Yuli mai kamawa.

Wannan matakin dai na rufe majalisar kamar yadda mai magana da yawun majalisar ta bayyana an dauke shi ne domin a ba dukkan 'yan majalisar damar gudanar da shagulgulan salla mai zuwa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng