Rayuka 2 sun salwanta a wani Rikicin 'Kungiyoyin Asiri da ya afku a Jihar Ebonyi

Rayuka 2 sun salwanta a wani Rikicin 'Kungiyoyin Asiri da ya afku a Jihar Ebonyi

Kimanin rayuka biyu suka salwanta a wani mummunan rikici da ya afku a tsakanin kungiyoyin asiri masu adawa da juna a yankin Ezzamgbo na karamar hukumar Ohaukwu ta jihar Ebonyi dake Kudu Maso Gabashin kasar nan ta Najeriya.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Nation sun bayyana cewa, yayin da wani mutum guda, Anselem Ifeanyi Omah ya riga mu gidan gaskiya a Yammacin ranar Talatar da ta gabata, rikicin ya sake salwantar da ran wani mai sunan Paul da aka harbe a daren ranar Laraba.

Legit.ng ta fahimci cewa, shekaru biyu kenan ana zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki na Ezzamgbo ba tare da wata tazoma da kungiyar asiri ba.

Rayuka 2 sun salwanta a wani Rikicin 'Kungiyoyin Asiri da ya afku a Jihar Ebonyi
Rayuka 2 sun salwanta a wani Rikicin 'Kungiyoyin Asiri da ya afku a Jihar Ebonyi

Bayan afkuwa rikici na musayar harsashan Bindiga a tsakanin kungiyoyin asiri, hukumar 'yan sanda ta samu nasarar cafke mutane takwas da ake zargin sa hannun su cikin kisan Anselem.

A yayin tabbatar da afkuwar wannan rikici, shugaban yankin na Ezzamgbo Clement Odah, ya bayyana da na sanin sa dangane da salwantar rayukan mutane biyu, inda yace cikin tsawon shekaru biyu da suka gabata ana zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da yake jagoranta.

KARANTA KUMA: Gwamna Al-Makura ya yafewa Fursunoni 35, ya Biya Tarar Mutane 28 a jihar Nasarawa

A yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata, Mista Odah ya nemi dukkanin jami'an tsaro dake da alhakin tabbatar da tsaro a yankin akan cafke duk wani wanda ake zargin sa hannun sa cikin wannan aika-aika tare da gurfanar da su da laifin kisan gilla.

Hakazalika kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar, Loveth Odah, ta bayar da tabbacin ta dangane da wannan rahoto inda ta ce hukumat za ta ci gaba da gudanar da bincike gami da titsiye wadanda suka shiga hannu a halin yanzu.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamna Umaru Tanko Al-Makura na jihar Nasarawa ya yafewa wasu Fursunoni 35 tare da sauke nauyin tarar da ke kan wasu mutane 28 da suka aikata kanana laifuka a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel