Kashe-Kashen Makiyaya: Kungiyar Miyetti Allah ta yi Barazanar shigar da 'Karar 'Yan Jarida masu 'Kage
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta yi gargadi da barazanar cewa, za ta dauki hukunci na Shari'a kan duk wani dan Jarida da kafofin watsa Labarai dake watsa rahotanni da suke muzanta 'yan Kabilar Fulani a fadin kasar nan ta Najeriya.
Shugaban Kungiyar na reshen jihar Nasarawa, Husseini Muhammad, shine ya yiwa wannan barazana sakamakon rahotanni dake yaduwa a kasar nan na Kisan jami'an 'yan sanda uku da kuma Manoma takwas a yankin Mararaba a jihar ta Nasarawa.
Legit.ng ta fahimci cewa, rahotanni da dama dake yaduwa a kasar nan na danganta makiyaya musamman Fulani da wannan aika-aika da makamansa da suka faru a Kasar nan.
A yayin mayar da martani dangane da wannan rahotanni da ake alakanta Makiyaya na Fulani da afkuwar kashe-kashe a Kasar nan, Alhaji Husseini ya bayyana cewa kungiyar sa a shirye take wajen shigar da karar duk wani dan Jarida ko kafar watsa Labarai da ta sake alakanta Fulani da wannan ta'addanci.
Yake cewa, "ina dalilin ambatar da kalmar Makiyaya Fulani a duk sa'ilin da aka kashe Mutane a kasar nan da hakan yake muzantawa 'yan kabilar Fulani tare da shafa masu bakin fenti ba tare da hakki ba. Saboda haka ba za mu sake lamuntar hakan ba"
"Kafofin watsa labarai su ke haddasa tsana da kuma ƙiyayya akan Al'ummar Fulani a kasar nan wanda lamari ya kai makura da sai mun shiga Kotu da duk wani dan jarida ko kafar watsa labarai da ta sake danganta mu da ta'addanci."
"Ko kadan ba ma goyon bayan duk wani Mutumin Fulani da aikata kaifin Kisa ko kuma tarayya cikin aikin ta'addanci. Jami'an tsaro su cafke duk wani mutumin Fulani da suka kama cikin wannan laifi."
KARANTA KUMA: Sabuwar Ranar Demokuradiyya: Wasu Shugabannin Najeriya sun yabawa Shugaba Buhari
"Sauran Kabilu kamar Al'ummar Neja Dalta sun kawo ta'addancin garkuwa da mutane a kasar amma ba bu wanda ambaton sunan su yayin da aka cafke wani mai garkuwa da Mutane sai dai sunan Fulani a duk sa'ilin da aka yi ta'addanci Kisa. Saboda haka ba za mu sake lamunta ba."
A sanadiyar haka ya sanya shugaban kungiyar ya ke gargadin maruwaita labarai akan ambatar kalmar Makiyaya na Fulani yayin da ta'addancin kisa ya afku a kasar nan, inda ya ce aikata hakan zai sanya su tafka gagarumin yaki a gaba Kotun Shari'a.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng