Hukumar 'Yan sanda ta Cafke 'Yan Fashi da Makami 4 tare da Muggan Makamai a jihar Enugu

Hukumar 'Yan sanda ta Cafke 'Yan Fashi da Makami 4 tare da Muggan Makamai a jihar Enugu

Wani sabon rahoto da sanadin shafin Jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta yi gagarumar nasara kan wasu 'yan fashi da makami a garin Nsukka dake Jihar Enugu a Kudanci kasar nan ta Najeriya.

Rahoton dai ya bayyana cewa, 'yan ta'addan 4 masu fashi da makami sun shiga hannun hukumar ta 'yan Sanda a yayin da suka fito aiki a babbar hanyar Nkpologu-Adani dake karamar hukumar Uzo Uwani a jihar ta Enugu.

Wannan rahoto ya zo ne da sanadin wata sanarwa ta Kakakin hukumar 'yan sanda na Jihar, SP Ebere Amaraizu, yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis din da ta gabata.

SP Ebere ya bayyana cewa, hukumar ta samu wannan gagarumar nasara ne kan miyagun da suka addabi masu ababen hawa da kuma al'umma mazauna wannan yanki na Uzo Uwani.

Hukumar 'Yan sanda ta Cafke 'Yan Fashi da Makami 4 tare da Muggan Makamai a jihar Enugu
Hukumar 'Yan sanda ta Cafke 'Yan Fashi da Makami 4 tare da Muggan Makamai a jihar Enugu

Kakakin ya kuma bayar da sunayen wannan 'yan ta'adda da aka cafke a ranar 31 ga watan Mayu kamar haka; Anthony Ogbobe, Chidera Eze, Chinedu Nwodo da kuma Onyebuchi Ugwuoke da suka fito daga yankuna daban-daban na jihar Enugu.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya sake sabunta Mukaman wasu Manyan Likitoci 2 na Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa, cikin gagarumar nasarar da hukumar 'yan sanda ta samu yayin cafke wannan miyagu, ta kuma cafke muggan makamai da dama masu hatsarin gaske.

A yayin haka kuma, kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Muhammad DanMallam, ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba jajircewa wajen dakile afkuwar miyagun laifuka a fadin jihar.

DanMallam ya kuma nemi al'ummar Jihar akan ci gaba da bayar da hadin ga hukumar da rahotanni da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a cikin jihar da kewayen ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel