'Yan bindiga sun sace wani ma'aikacin INEC a wata jiha

'Yan bindiga sun sace wani ma'aikacin INEC a wata jiha

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani jami'in hukumar zabe ta kasa a jihar Akwa Ibom

'Yan bindiga sun sace wani ma'aikacin INEC a wata jiha
'Yan bindiga sun sace wani ma'aikacin INEC a wata jiha

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani jami'in hukumar zabe ta kasa a jihar Akwa Ibom.

Majiyarmu Legit.ng ta samu rahoton cewa an sace jami'in ne a ranar Talatar nan data gabata a kusa da wata makarantar Firamare ta gwamnati, Oruk Atah 2, a karamar hukumar Ukanafun ta kan babbar hanyar Ukanfun Azumini, inda jami'in mai suna Otobong Ukpong, yake kan hanyar shi ta zuwa ofis.

DUBA WANNAN: Sama da mutane 1,000 sun canja sheka daga PDP zuwa APC

Wani dan uwa ga jami'in, mai suna Mbetobong Sylvester Ukpong yace, "An sace Dan uwan nashi a Uruk Ata 2, da safiyar ranar Talata, 5 ga watan Yuni, a hanyar shi ta zuwa aiki ofishin su na INEC dake Ukanafun." Uruk Ata 2, wuri ne da 'yan daba da 'yan bangar siyasa suka samu gurin zama, inda suke yin mutane ciki kuwa harda wasu manyan malaman coci mutum hudu da suka yi garkuwa dasu a kwanakin baya, sannan sun kona gidaje da kuma kashe mutane guda hudu kwanan nan."

Yace Dan'uwan nashi, wanda shine autan gidansu, daga kauyen Iwukem dake karamar hukumar Etim Ekpo dake jihar, yana kan hanyar shine ta zuwa rabon katin zaben.

Mbetobong yace wadanda suka sace shi din sun kira iyalan shi suka ce suna bukatar naira miliyan 10, inda yace duk danginsu bazasu iya biyan kudin ba.

"Sun nemi da mu biya naira miliyan 10, sun kirane ta wayar dan uwan nawa. Amma dangin mu sunce bazasu iya biya ba."

Mai magana da yawun yan sandar jihar, DSP Odiko Macdon, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace, mun samu rahoton, mun kuma tabbatar da hakan. Amma 'yan sanda suna iya bakin kokarin su akan matsalar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: