Fadar shugaban kasa tayi wa majalisa kunnen uwar shegu
Fadar gwamnatin tarayyar Najeriya tayi kunnen uwar shegu da bukatun da majalisar Najeriya ta aikowa shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda tace a yanzu ba zata mayar da wani martani ba dangane da sharudan da Majalisar ta gindayawa shugaban kasar
Fadar gwamnatin tarayyar Najeriya tayi kunnen uwar shegu da bukatun da majalisar Najeriya ta aikowa shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda tace a yanzu ba zata mayar da wani martani ba dangane da sharudan da Majalisar ta gindayawa shugaban kasar.
DUBA WANNAN: Fashin Offa: An kara kama wasu yaran Saraki guda 2
Majalisar dai ta gindayawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu bukatu har guda 12, bayan da Majalisar ta yi wani zama akansa kuma take bukatar shugaban kasar ya aiwatar da su ko kuma su saka kafar wando daya shi.
Kakakin fadar shugaban kasar Najeriyan Malam Garba Shehu, tun a farko ya bayyana cewa ba zasu yi wata magana akan batun ba a yanzu, sai dai kuma watakila a nan gaba suyi. Amma jam’iyyar APC ta fito fili ta bayyana cewa tana daukar mataki na kawo sulhu tsakanin bangarorin guda biyu.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen arewa maso yammacin Najeriya, Inuwa Abdulkadir, ya fadawa Muryar Amurka cewa a jam’iyyance jam’iyya ta siyasa itace uwa, itace uba ga duk wani dan takara, saboda haka dole ne jam’iyyar ta dauki mataki don tabbatar da cewa an sasanta lamarin.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng