Shugaba Buhari ya sake sabunta Mukaman wasu Manyan Likitoci 2 na Najeriya
Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sabun ta mukaman wasu sabbin daraktoci na wasu manya asibitoci biyu na Kasar nan.
Shugaba Buhari sabunta mukamin Dakta Jafaru Alunua Momoh a matsayin darakta na Asibitin Kasa dake Birnin Abuja da kuma Dakta Nwadinigwe Cajetan Uwatoronye a matsayin darakta na babban Asibitin 'Kashi na Kasa dake jihar Enugu.
Legit.ng ta fahimci wannan shine karo na biyu da Dakta Jafaru ke rike da wannan mukami inda sabon nadin na sa zai fara daga ranar 5 ga watan Yuli mai gabatowa.
A yayin haka kuma, mukamin Dakta Uwatoronye zai fara ne daga ranar 30 ga watan Mayun 2018 wanda wannan shine karo na karshe da zai rike mukamin sakamakon yadda dokokin kasar nan suka shar'anta.
Wannan sanarwa ta zo ne da sanadin Misis Boade Akinola, Kakakin Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole, ta bayyana cikin wani sako na son barka da ta yiwa Manyan Likitocin biyu.
KARANTA KUMA: Barazanar Banza ce Kawai - Matasan Jihar Edo ga Majalisar Dokoki ta Tarayya
Misis Boade ta gargade su akan ci gaba da jajircewa tare da adalci wajen saukin nauyin da rataya a wuyansu, inda ta bayyana cewa sai an gwada akan san na kwarai din da suka nuna ya sanya suka cancanci wannan sabunta ta mukaman su.
Ta kara da cewa, wannan sabunta mukaman da suka samu zai dabbaka alaka mai karfin gaske tsakanin su da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen inganta hakokin kiwon lafiya ga al'ummar Najeriya baki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng