Gwamnatin Tarayya ta tsawaita izinin Hutun Haihuwa zuwa Watanni 4 a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita izinin Hutun Haihuwa zuwa Watanni 4 a Najeriya

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito mun samu rahoton cewa, gwamnatin tarayya ta tsawaita samun izini na hutun haihuwa ga Ma'aikatan Mata a kasar nan ta Najeriya daga watanni uku zuwa hudu.

Tuni dai Gwamnatin Najeriya ta haramta sallamar Mata daga bakin aikin su a yayin da suke dauke da juna Biyu ko kuma wasu ababe da suke shafi rayuwar su ta aure a gidan Miji.

Ministan kwadago da aikace-aikace na Najeriya, Chris Ngige, shine ya bayyana hakan yayin taron Cibiyar kwadago ta Duniya da aka gudanar a Birnin Geneva na Kasar Switzerland.

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita izinin Hutun Haihuwa zuwa Watanni 4
Gwamnatin Tarayya ta tsawaita izinin Hutun Haihuwa zuwa Watanni 4

Yake cewa shimfidar dokoki ta tilastawa ma'aikatu a Najeriya su baiwa Mata rangwami da dama ta saukaka ma su aiki a yayin da suke shayarwa.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari da Ministocin sa sun yi Bankwana da Fayemi yayin Zaman Majalisa

Ya ci gaba da cewa, cikin kowane nau'i na aiki a Kasar nan gwamnatin tarayya ta tsawaita samun izinin daukar hutu daga makonni 12 zuwa 16 ga Ma'aikatan Mata da suka haihu domin samun isashen lokaci na watstsakewa ga uwa da kuma jaririn ta musamman a bangaren shayarwa.

Ministan ya kara da cewa, dole ne a baiwa Ma'aikatan Mata damar wawalwa da samun sukuni a yayin da su ka haihu, inda ya ce wannan doka ba ta takaita kadai akan Ma'aikatun Gwamnati ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel