Shari'a sabanin hankali: An tura su gidan kaso na wata tara-tara saboda sun saci wayar wuta
A ranar Larabar nan ne wata Kotu a Minna babban birnin jihar Neja ta yankewa wasu mutane biyu data kama da laifin satar wayar wuta, hukuncin daurin wata tara - tara a gidan kaso
A ranar Larabar nan ne wata Kotu a Minna babban birnin jihar Neja ta yankewa wasu mutane biyu data kama da laifin satar wayar wuta, hukuncin daurin wata tara - tara a gidan kaso. Alkalin kotun, Jibrin Zabo ya yankewa Mohammed Alhaji da Jamilu Isa hukuncin, inda ya bayyana kama su da aikata laifuka guda uku, laifin aikata ta'addanci, karya doka da kuma sata. Alkalin ya bukaci wadanda ake zargin da su biya naira dubu talatin - talatin.
DUBA WANNAN: Dan damfara ya damfari hukumar EFCC a yanar gizo
Dan sandan da ya kawo masu laifin Insp. Ahmed Ali, ya bayyanawa kotu cewar jami'an 'yan sanda ne suka kama masu laifin suka kawo su ofishin 'yan sanda na Kpakungu dake garin Minna a ranar 1 ga wannan watan.
Ali ya bayyana cewar sun haura gidan wani mutum mai suna Abdulfatai Jimoh suka dauke mishi wayar wuta.
Ya kara da cewar laifin su dai dai yake da sashi na 97,343 da kuma sashi na 288 na dokar kasa.
Da aka karantowa masu laifin laifukansu basu musanta ba, inda suka roki kotu data yi musu sassauci.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng