Dalilin da yasa na watsa wa mahaifin yara na tafasashen ruwa - Wata mata

Dalilin da yasa na watsa wa mahaifin yara na tafasashen ruwa - Wata mata

Rundunar Yan sanda ta jihar Legas damke wata mace, Joy Imeribe mai shekaru 32 saboda ta watsa wa saurayinta Ike Akachi tafasashen ruwa wanda hakan ya yi masa mummunan rauni a jiki.

Wanda ake zargi ta shaidawa yan sanda cewa abin ya faru ne a ranar 29 ga watan Mayu bayan sunyi ca-can banki da Mr. Akachi a gidansu da ke Ijesha.

Kamar yadda ya ke a bayanin da Imeribe tayi wa yan sanda, ta ce sun sami rashin jituwa da dadare kuma ta kwanta barci da haushin saurayinta.

Bayan ya gari ya waye, budurwar ta tafasa ruwa rabin bokiti kuma ta antayawa saurayin lokacin da ya ke kokarin dafa abincin da zai karya da shi wanda hakan ya yi masa rauni sosai.

Dalilin da yasa na antayawa saurayina tafasashen ruwa - Wata matashiya
Dalilin da yasa na antayawa saurayina tafasashen ruwa - Wata matashiya

KU KARANTA: Kishi ya saka wata mata yi wa kishiyar ta wanka da tafasashen ruwa

Ms Imeribe ta ce ba da gan-gan ta watsa wa saurayin na ta ruwan zafin ba, inda ta kara da cewa ainihi ta tafasa ruwan zafin ne don yiwa yaransu wanka.

"Abinda ya janyo fadan shine na fita zuwa kasuwa don in siyo tufafin gwanjo daga kasuwar Yaba wanda zan sayar a Aswani.

"Bayan na dawo gida, ya tambaye inda na tafi kuma na fada masa amma sai ya ce in koma inda na fito. Ban amsa shi ba sai dai ya kama ni da fada misalin karfe 4 na yamma.

"Ya yi min duka, ya daure ni a gado, ya rika fizgar gashi na kuma yana ja na a kasa sannan daga baya ya kulle ni a daki. Ya dade yana min hakan. Shine kuma da safe, ya sake taso da rikicin, ina da juna biyu na wata daya saboda haka sai na watsa masa ruwan zafin don in kare kaina," inji matar.

Kwamishinan Yan sanda na jihar Legas, Imohimi Edgal ya shawarci dukkan wanda suke fuskantar matsi da takura a gidanjensu su rika kai kara ofishin yan sanda don kiyaye afkuwar lamari irin wannan.

Mr Edgal ya ce za'a gurfanar da matar a gaban kuliya idan an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164