Jirgin sama dauke da mutane 10 ya yi ɓatan dabo a sararin samaniya
Al’ummar kasar Kenya na cikin zullumi biyo bayan bacewar wani jirgin sama dake dauke da akalla mutane goma a sararin samaniya tun a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni,inji rahoton jaridar The Cables.
A yau Laraba, 6 ga watan Yuni ne ake sa ran hukumomi zasu cigaba da farautar jirgin, wanda ya tashi daga garin Kitale zuwa babban filin sauka da tashin jirage na Jomo Kenyatta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Alhinin rabuwa: A yau marigayi Ado Bayero ya cika shekaru 4 da rasuwa
“Jami’an kwana kwana suna bazama neman jirgin wanda yayi batan dabo, amma har yanzu babu wani labari.” Inji kamfanin jirgin, mai suna Fly Sax. Sai dai iyalan fasinjojin jirgin sun koka kan yadda kamfanin bata basu wani muhimmin bayani ba.
Guda cikin yan uwan daya daga cikin fasinjojin jirgin mai suna Abdi Ali, Mohamed Abdi ya bayyana cewa: “Mun samu labari suna neman jirgin, yayin da mu kuma muna wani Otal, ina ganin kamfanin bata bamu wani muhimmin bayani ba, abinda nake so kawai shi ne su bamu gawan yan uwanmu mu binne su.
Sai dai hukumar kare bala’o’I na kasar Kenya ta bayyana cewar tana iya bakin kokarinta, musamman a yankin Ndakini, inda ake zaton jirgin ya sauka, amma sakamakon daji ne wajen, jirgi mai saukan angulu baya gani da kyau, inji jami’in hukumar, Pius Masai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng