Har ila yau: Abdulmumin Kofa ya kara fadawa tsaka mai wuya a majalisar wakilai, an fara tuhumar sa
Majalisar wakilai ta bukaci kwamitin tan a da da’a da labara da ya binciken kalaman mamba mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji a jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa wasu kalamai da ya yi a jiya, Talata, bayan zaman majalisar na hadin gwuiwa.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan mamba daga jihar Kogi dan jam’iyyar PDP, Sunday Karimi, ya jawo hankalin majalisar a kan wasu kalaman Kofa da ya yi a madadin ‘yan majalisar masu goyon shugaba Buhari.
KU KARANTA: Mazauna wani kauye a Filato sunyi wa makiyaya mummunar ta'asa
A jiya ne bayan ganawar gaggawa ta hadin gwuiwa tsakanin majalisar dattijai da ta wakilai, Kofa, ya bayyana cewar basa tare da wasu ‘yan majalisar da ake zargi da kulle-kullen tsige shugaba Buhari tare da nisanta kan su daga wannan Magana.
Kofa ya bayyana cewar mafi yawa daga cikin ‘yan majalisar da suka yi magana yayin ganawar su ta sirri a jiya, ‘yan jam’iyyar adawa ne ta PDP tare da bayyana cewar ‘yan majalisar jam’iyyar APC na shakkar bayyana ra’ayin su duk da kasancewar shugabannin majalisun ‘yan jam’iyyar APC ne.
Majalisar ta zargi Kofa da kokarin kawo rudani tare da bayar da bayanan karya ga jama’a da niyyar haifar rashin jituwa tsakanin shugabancin majalisu da bangaren zartarwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng