Yanzu Yanzu: Hukumar EFCC ta gurfanar da mataimakin gwamnan jihar Bauchi da wasu mutane 4 a gaban kotu (hotuna)
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Babayo Garba Gamawa, tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Aminu Hammay da wasu mutane uku zasu gurfana gaban kotu.
Za’a gurfanar da su ne a gaban babban kotun tarayya dake jihar Bauchi a safiyar yau Laraba, 6 ga watan Yuni.
Mai shari’a Justis M. Shitu ne zai saurari shari’arsu.
KU KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban kasa baiyi umurnin sallaman kowani jami’i daga ofishin amnesty ba – Fadar shugaban kasa
Hukumar EFCC shiyar Gombe na tuhumarsu da laifuka biyar wanda suka hada da satar kudi da ya kai kimanin naira miliyan 500.
Idan bazaku manta ba a baya Legit.ng ta kawo maku yadda hukumar ta EFCC ta dunga gurfanar da tsoffin gwamnoni musamman daga yankin arewacin kasar bisa zargi da ake yi musu na satar kudi a lokacin da suke kan mulki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng