Wasu 'Yan sanda 3 zasu fuskanci zazzafan hukunci 
 bayan da aka kama su suna Caca

Wasu 'Yan sanda 3 zasu fuskanci zazzafan hukunci bayan da aka kama su suna Caca

- 'Yan sanda zasu fara fuskantar hukuncin da ake yiwa sauran jama'a idan an kama su suna Caca

- Amma sai idan an kama su suna Cacar ne alhali suna bakin aiki

- Yanzu haka har an damke biyu daga cikinsu kuma suna shirin fuskantar hukunci

Kwamishinan Ƴan sanda na jihar Legas Imohimi Edgal ya ce duk wani jami'in rundunar da aka kama yana Caca alhali yana bakin aiki zai fuskanci hukunci mai tsananin da zai haɗa da ladaftarwar ragin mukami ko kuma kora baki ɗaya.

Wasu 'Yan sanda 2 zasu fuskanci zazzafan hukunci 
 bayan da aka kama su suna Caca
Wasu 'Yan sanda 2 zasu fuskanci zazzafan hukunci bayan da aka kama su suna Caca

Kwamishinan ya shaida hakan ne a wani jawabi da kakakin rundunar na jihar Legas ya ya fitar a jiya Talata.

Imohimi ya kuma buƙaci jama'a fa su kai rahotan duk wasu halaye na banza ko kuma rashin bin dokar aiki da wasu baragurbi daga cikin Ƴan sanda ke yi.

Wannan gargadi dai yana zuwa bayan da rundunar ta damke wasu jami'anta uku suna Caca alhali suna bakin aiki.

KU KARANTA: Karanta mummunan matsalar da shan kwaya ya janyo tsakanin Saurayi da Budurwa

Jami'an da ba'a bayyana sunansu ba yanzu haka suna fuskantar hukuncin ladaftarwa da ka iya zama na rage muƙami ko kora baki ɗaya, jawabin ya bayyana.

Kakakin rundunar ya shaida cewa taun farko dai an jawo hankalin rundunar ne kan yadda wani bidiyo da aka saka a shafin sadarwar zamani ya nuna yadda jami'an su biyu sun share wuri suna ta Caca bayan sun gama karbar na goro a hannun ƴan kabu-kabu.

Wasu 'Yan sanda 2 zasu fuskanci zazzafan hukunci 
 bayan da aka kama su suna Caca
Wasu 'Yan sanda 2 zasu fuskanci zazzafan hukunci bayan da aka kama su suna Caca

Bidiyon dai an sanya shi ne a kafar Instablog tare da rubutawa a jikinsa cewa, yadda Ƴan sandan suka yada zango a kusa da Bankin Zanith dake kan titin Opebi a Legas suna ƙirga cin hancin da suka karba sun kuma kunna tabarsu suna zuka.

Amma bayan fara bincike ne sai rundunar ta gano cewa ba kudi suke ƙirgawa ba Caca suke yi kalar wata wadda tayi kaurin suna da Baba Ijebu.

Mr Oti ya ce, ganin wancan bidiyon ne ya sanya nan take Kwamishinan ha bayar da umarnin a kame jami'an domin tsare su tare da kuma hukunta su.

"Yanzu haka jami'an suna fuskantar hukuncin ladaftarwa da ka iya zama ɗan biyu; rage muƙami ko kuma kora baki ɗaya". A cewar Kakakin

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng