Yan haya sun tsere da yaran maigidansu 2 a Edo
Wasu masu haya biyu da aka ambata da suna Mercy da Rose sun tsere da yaran mai gidan su guda biyu a kauyen Utese dake karamar hukumar Ovia North East.
An bayyana sunayen yaran a matsayin Amada mai shekaru hudu da Christable mai shekaru biyu.
An rahoto cewa mahaifiyarsu ta ba matan aiyen yaran kafin ta tafi wanke kaya a kogi.
Masu hayan wanda aka ce sun fito daga jihar Cross River sun tare ne a garin makonni uku da suka shige sannan kuma sun fadama mai gidan nasu cewa daya na aiki a gona yayinda dayar ta kasance mai gyaran gashi.
An tattaro cewa an balle kofar dakinsu inda aka gano cewa sun kwashi wasu daga cikin kayayyakinsu sannan suka tsere.
Mazauna unguwan sun bayyanawa iyayen yaran cewa sun ga mutanen suna tsayar da motoci a babban titi amma sun zata fita zasuyi da yaran kamar kullun.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Hukumar EFCC ta gurfanar da mataimakin gwamnan jihar Bauchi da wasu mutane 4 a gaban kotu (hotuna)
Mahaifiyar yaran Faith Osaruoname ta bayyana cewa ta saba barin yaran tare da mutanen a duk lokacin da zata fita unguwa.
Ta kuma bayyana cewa bata san komai game das u ba kuma bata da hoton mutanen.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng