An fifita Jihohin Kano da Katsina wajen daukar Ma'aikatan 'Yan Sanda

An fifita Jihohin Kano da Katsina wajen daukar Ma'aikatan 'Yan Sanda

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta dauki sababbin Ma’aikata sama da 5, 000 kwannan nan a fadin kasar. Sai dai bincike ya nuna cewa Jihohin Arewacin Kasar ne su ka fi samun kaso-mafi-tsoka na wadanda aka daukan.

An fifita Jihohin Kano da Katsina wajen daukar Ma'aikatan 'Yan Sanda
Sufeta Janar na 'Yan Sandan Najeriya Ibrahim K. Idris

Akalla mutane 37, 000 ne su ka nemi aikin ‘Dan Sanda sai dai wadanda su ka dace ba su kai kashi 15% cikin 100 ba kamar yadda jerin da aka fitar ya nuna. Mun ji cewa a cikin wadanda aka dauka sama da mutum 300 duk sun fito ne daga Jihar Kano.

Har wa yau Jaridar The Cable ta bi diddiki inda ta gano cewa an dauki mutm 228 a Jihar Katsina inda nan ne Mahaifar Shugaban Kasa. A takaice dai a Yankin Arewa-maso-Yamma, an dauki akalla mutum 1300 daga cikin 5233 da aka dauka.

KU KARANTA: Labari da dumi-dumi: Shugaban Kasa Buhari yayi wani muhimmin nadi

Yankin Arewa ta tsakiya na da mutum 823 ne a cikin sababbin ‘Yan Sandan da aka dauka. Haka kuma an dauki mutum 759 ne a Yankin Arewa a gabas. Kashi 55% dai na wadanda su ka samu aikin na ‘Dan Sanda sun fito ne daga Arewacin Kasar.

A kaf Yankin Kudu maso Gabas an dauki mutum 651 inda a Kudu maso Yamma kuma aka samu mutum 921. Jihar Oyo ce ta zo ta 3 a jerin idan aka duba Jihohin da su ka caba, an dauki mutum 225 yayin da Birnin Tarayya Abuja ta samu mutum 42 kacal.

Yanzu dai an fitar da cikakken jerin na sababin ‘Yan Sanda inda za a ga cewa mutum 779 su ka samu shiga daga Yankin Kudu ta Kudu watau Neja-Delta. Yanzu haka dai ana shirin tantance sababbin Jami’an na ‘Yan Sanda da aka dauka aiki a fadin Kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng