Da gan-gan na sa mata rawan Shaku Shaku da hijabi a waka na – Falz ya maida martani ga MURIC
Ana ci gaba da kace nace akan wakar Shaku Shaku da akayi inda aka nuno mata sanye da hijabi suna rawar fitsara.
Mawakin da ya shirya wannan bidiyon mai suna Folarin Falana inda ake yi masa inkiya da Falz yayi tsokaci akan lamarin bayan gargadi da kungiyar kare hakkin Musulmi tayi masa na ya janye wakar.
A cewar mawakin da gan-gan ya sanya mata wannan rawa sanye da hijabi domin a cewarsa abubuwan dake faruwa a kasar na ci masa tuwo a kwarya.
Ya ce: “Da gan-gan nayi. Muna cigaba da mantawa ko ince watsi da yara matan da basu san komai ba sannan saboda dukka lamuran da muke fuskanta, sace-sacen mutane da kashe-kashe musamman a yankin arewacin kasar, yan matan Chibok da na Dapchi, abun damuwa ne sannan kuma bamu yawan magana akansu kuma nayi mamaki da naji mutane na fadin menene dalilin da yasa ka sa mata sanye da hijabi rawan Shaku Shaku... Shin akwai wani aibu a cikin mutane na rawa saboda sun hijabi? Shin akwai wata doka da yayi hani akan haka?"
A halin da ake ciki kungiyar kare hakkin musulmi ta bayyana wannan bidiyo a matsayin cin zarafin Musulmi da Fulani.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daraktan Kogi ya fadi ya mutu a Ofis
Sannan kuma ta bayar da wa’adi kan ayi gaggawan janye bidiyon daga kasuwa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng