Yanzu Yanzu: Ana nan ana tattara sa hannu don tsige shugaba Buhari a yanzu haka – Dan majalisa
Wani dan majalisar wakilai Muhammed Gudaji Kazaure, yayi zargin cewa ana nan ana shirya makirci don tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Vanguard ta rahoto cewa dan majalisar wanda keda kusanci da shugaba Buhari a majalisar ya bayyana hakan a ranar Talata, 5 ga watan Yuni bayan ganawar sirri na sa’o’i 3 tsakanin majalisar dattawa da na wakilai.
Yayi ikirarin cewa an tattara sa hannu domin tsge shugaban kasar amma yana da tabbacin cewa barazanar ba zai cimma nasara ba saboda wadanda ke bayan shugaban kasar suna da yawa.
KU KARANTA KUMA: Kalli yadda ake rabon abinci karkashin tsarin ciyar da yara na gwamnatin tarayya a wata makarantar firamarin Jihar Kano
Kazaure yace shi baya goyon bayan abunda ya bayyana a matsayin makirci don tsige shugaban kasar idan yaki amincewa da sharudan da aka gindaya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng