Kasar Jamus za ta Yaso 'Yan Najeriya 30, 000 da suka yi Gudun Hijira

Kasar Jamus za ta Yaso 'Yan Najeriya 30, 000 da suka yi Gudun Hijira

Da sanadin shafin Jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, Gwamnatin Kasar Jamus ta kammala shiry-shiryen ta tsaf domin taso keyar kimamin 'yan Najeriya 30, 000 da suka yi gudun hijira dake neman mafaka a Kasar ta.

Babbar hadima ta musamman ga shugabn Kasa Muhammadu Buhari akan harkokin kasashen ketare, Honarabul Abike Dabiri Erewa, ita ce ta bayyana hakan yayin wani shiri akan yin haure da hijira da aka gudanar a babban birnin kasar nan na Abuja.

A cewar ta, dalilan da mafi akasarin 'yan Najeriya suka bayar na neman mafaka a kasar Jamus ya sabawa tushe na gaskiya, yayin da wasu daga yankunan Yamma da Gabashin Najeriya suka ce ai rikicin Boko Haram ya sanya su ka yi kaura.

Abike Dabiri Erewa
Abike Dabiri Erewa

Cikin jawaban na ta na ranara Talata ta yau, Abike ta bayyana cewa wasu 'yan Najeriyar dake neman mafaka a kasar ta Jamus sun bayar da dalilai na cewar su na fama da tawayar hakkin su a kasar nan a yadda ba su iya soyayyar su auren jinsi.

Sai dai babbar hadimar ta bayyana cewa, kawowa yanzu kasar ta Jamus ba ta kayyade ranar dawo da 'yan Najeriyar gida sakamakon rashin tabbas na cika masu burikan da suka kudirta.

KARANTA KUMA: Yara 152m ke Aikin 'Kwadago duk Shekara a fadin Duniya - ILO

Legit.ng ta fahimci cewa, irin wannan gudun hijira da ta sabawa ka'ida ba ta tushen zama a yayin da kasashen ketare ke fama da na su matsalolin da kalubalai na karan kansu.

Ta kara da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta na ci gaba da taka rawar gani wajen magance ire-iren wannan hijira da ta sabawa ka'ida da 'yan Najeriya keyi, inda ta ce gwamnatin ta na ci gaba da yakar rashawa, rashin tsaro da kuma kokarin ta na bunkasa tattalin arziki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng