Wane mutum: Shugaban Kasa Buhari ikon Allah ne Inji wani babban Sanata

Wane mutum: Shugaban Kasa Buhari ikon Allah ne Inji wani babban Sanata

- Ahmad Lawan yace tafiyar Buhariyya ta wuce batun Shugaba Buhari

- Sanatan na APC yace tafiyar Buhari dai ta kunshi gaskiya da amana

- ‘Dan Majalisar ya yabawa Buhari na kawo karshen ‘Yan Boko Haram

Mun samu labari daga Daily Trust cewa Sanatan Yobe na Yankin Arewa wanda shi ne shugaban masu-rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya Ahmad Lawan yace maganar Shugaba Muhammadu Buhari ya zama wani abin dabam.

Wane mutum: Shugaban Kasa Buhari ikon Allah ne Inji wani babban Sanata
Sanata Ahmad Lawan yace Buhariyya tafiya ce ta gaskiya

Sanatan na Jam’iyyar APC mai mulki Ahmad Lawan yake cewa tafiyar Shugaba Buhari ya tashi daga mutum guda ya zama wata tafiya. Ahmad Lawan yace idan aka ce Buhari ana maganar tafiya da tsari na gaskiya da rikon amana.

KU KARANTA: Majalisa na neman tsige Shugaban Kasa Buhari

Ahmad Lawan a lokacin da ya gana da Kungiyar NEYCPB na Magoya bayan Shugaban Kasa Buhari da ke Arewa-maso-Gabas yace Shugaban Kasa Buhari bai shigo siyasa da niyyar satar kudin Gwamnati ba don haka sai a dafa masa.

‘Dan Majalisar dai yake cewa Shugaban Kasar na bukatar taimakon sauran Jama’an kasar nan don kuwa a cewar sa babu wanda zai iya mulkin Najeriya ba tare da goyon bayan sauran al’umma ba saboda mugun sarkakiyar Najeriya.

Dr. Ahmad Lawan dai ya yaba da kokarin da Shugaba Buhari yayi daga hawan sa mulki kawo yanzu na maganin ‘Yan ta’addan Boko Haram a Arewacin Kasar. Kungiyar ta NEYCPB dai ta nada Sanata Ahmad Lawan a matsayin Uban ta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng