Mutanen dake kewaye da shugaba Buhari mahaukata ne – Sheikh Gumi
Wani malamin addinin Musulunci mai ra’ayin rikau dake jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya zargi shugaba Buhari da kewaye kan sa da mashawarta marasa ilimi kuma marasa tausayi.
Gumi na wadannan kalamai a matsayin martini ga nuna hoton tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Mukhtar Yero, dauke da allon rubutun laifukan da ake tuhumar sa da su bayan hukumar EFCC ta gurfanar das hi gaban kotu ranar Alhamis da ta wuce.
Gumi ya bayyana cewar binciken da ake yiwa wasu tsofin gwamnoni a kasar nan, ra’ayin wasu masu bas hi shawara ne da basa tare da mutane.
“Sam basa tare da mutane. Sun kulle shugaban kasa, sun hana kowa ganin sa balle a gaya masa gaskiya,” a cewar sheikh Gumi.
Sannan ya kara da cewa, “duk cikin su ban ga mai hankali ba, ku gayamin idan da mai hankali a cikin su, ba wanda cikin su zai iya gaya masa gaskiya.”
DUBA WANNAN: Duba hotunan wani magidanci da ya yiwa wata yarinya mai shekaru 5 fyade
Gumi, a cewar sa, kuskure ake binciken tsofin gwamnoni tare da tona masu asiri, yana mai bayyana yin hakan da bin shawarar jahilai da shugaba Buhari ke yi tare da bawa shugaban kasa shawarar ya yafewa dukkan tsofin gwamnoni tare da yin kira gare su da su gyara halayen su, su zama masu gaskiya.
A cewar sheikh Gumi, Buhari zai kai kan sag a halaka muddin ba fada masa gaskiya a kan kuskuren da yake aikatawa na binciken tsofin gwamnoni ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng