Maza ayi hattara: Yadda wata Malama ta burma ma Maigidanta wuka daga cacar baki
Wata Malamar makarantar Firamari a jihar Legas ta hallama Maigidanta ta hanyar burma masa wuka, bayan wani dan sa’insa da suka samu wanda har ta kai su ga cacar baki, kamar yadda jaridar DailY Trust ta ruwaito.
Har yanzu Yansandan jihar Legas na tsare da Malamar mai suna Bukola, inda suke gudanar da binciken kwakwaf don tabbatar da gaskiyar lamarin, kafin su garzaya ga Kotu.
KU KARANTA: Ga Buhari ga Atiku: Ministan Buhari ta yi tsayuwar gwamen Jaki
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewar Bukola ta burma ma mijin nata wuka ne a ranar Laraba a yayin fada da ta kaure a tsakaninsu, a gidansu dake unguwar Igbogbo cikin yankin Ikorodu na jihar, inda ta dauki wukar da nufin kare kanta, amma aka samu akasi ta luma masa ita a ciki.
Sai dai wani makwabcin ma’auratar ya bayyana cewa Bukola ta sha fama da cin zarafi da cin zali daga wajen mijinta a baya, wanda ta kai ga iyayenta sun nemi a kashe auren, amma Matar tace atabau tana son Mijinta a haka, balle kuma suna da yara biyu.
Bugu da kari wata makwabciyarsu mai suna Adeolu tana cewa bayan samun labarin da ya faru, basu yi wata wata ba suka garzaya da Mijin Bukola zuwa Asibiti, amma bai kai labari ba, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng