Landan, New York da wani Gari ne aka fi samun masu kudi a Duniya
Mun kawo maku jerin Biranen da a Duniya yanzu babu inda su ka kai su yawa masu kudi. Knight Frank da ke Birnin Landan tayi wannan bincike a bana. Idan aka ce masu kudi ana nufin wadanda su ka ba Dala Miliyan 1 baya.
Ga dai jerin Garuruwan nan kamar haka:
1. Landan
Duk Duniya babu Garin da ke dauke da Attajirai rututu irin Birnin Landan da ke cikin Kasar Ingila. Akwai Attajirai sama da 350, 000 a cikin Landan.
2. New York
Bayan Landan kuma sai Birnin New York na Kasar Amurka a baya. A Birnin na New York ana tunani akwai masu kudi kusan 340, 000 a yanzu.
3. Tokyo
Babban Birnin Kasar Jafan watau Tokyo ne na 3 a wannan jeri. Tokyo mai mutum sama da Miliyan 13 na dauke da Attajirai kusan 280, 000.
4. Hong Kong
Garin Hong Kong da ke Kudancin Kasar Sin na cikin manyan Biranen Duniya. Akwai manyan Attajirai akalla 220, 000 a Birnin Hong Kong.
5. Singapore
Garin Singapore da ke Kudancin Kasar Malaysia a Nahiyar Asiya ne na 5 a wannan jeri. Binciken ya nuna cewa akwai masu kudi fiye da 210, 000 a Birnin.
Bayan wadannan Garuruwa dai akwai irin su Bejin, Cikago, Los Anjelos da sauran su wadanda ke dankare da Attajirai a Duniya.kamar yadda binciken da aka yi a shekarar nan da nuna.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng