Za mu dauki gandurobobi aiki saboda magance matsalolin gidan yari – Dambazau

Za mu dauki gandurobobi aiki saboda magance matsalolin gidan yari – Dambazau

- Kwanaki wasu mutum sama da 200 su ka tsere daga gidan yari a Neja

- Ministan harkokin cikin gida yace dai rashin Ma’aikata ya jawo hakan

- Dalilin wannan Gwamnatin Buhari za ta dauki gandurobobi 6000 aiki

Mun samu labari cewa Ministan harkokin tsaro na cikin gida watau Abdulrahman Dambazzau ya bayyana shirin da ake yi na daukan Matasa har 6000 da za su yi aiki a gidajen yarin Kasar.

Za mu dauki gandurobobi aiki saboda magance matsalolin gidan yari – Dambazau
Minista Dambazau yace za a kara yawan Ma'aikatan gidan kaso

Janar Abdulrahman Dambazzau mai ritaya ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari za ta kara kaimi wajen tsare gidajen yari don haka za a kara daukar Ma’aikata da dama. Ministan ya bayyana wannan ne lokacin da ya kai ziyara Garin Minna.

Idan ba ku manta ba kwanaki wasu su ka tsere daga wani gidan Yari da ke Minna a cikin Jihar Neja. Ministan yace daga cikin mutum 210 da su ka tseren dai an yi nasara kama 28 yanzu haka, yayin da har yau ana neman sauran 182 ruwa-a-jallo.

KU KARANTA: An gano inda tukwanen da Jonathan ya saya su ka shige

Ministan Kasar yace idan aka kara daukar Ma’aikatan gidan kaso za a samu saukin tserewa da ake yi daga gidajen yari. Janar Dambazzau yace a halin yanzu Gwamnati na fama ne da karancin Ma’aikata a gidajen yarin Kasar kuma za a gyara.

Game da wadanda su ka tsere daga gidan mazan dai Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Neja Dibal Yakadi yace an baza Jami’an ‘Yan Sanda rututu a tashoshin mota a Jihar domin gano masu laifin. Hukuma na sa ran a sake yin ram da su.

Kwanaki kun ji cewa duk da Sojojin da aka baza a Jihar Zamfara har yanzu ba a samu saukin kashe-kashe ba. Kwanan nan dai aka kashe mutane akalla 15 a Kauyen Zakuna da ke cikin Garin Anka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel