Wata Annoba ta hallaka daliba 1, ta kwantar da 40 a kwalejin yan Mata na Kaduna

Wata Annoba ta hallaka daliba 1, ta kwantar da 40 a kwalejin yan Mata na Kaduna

Akalla dalibai 40, arba’in ne aka garzaya dasu asibiti da gaggawa cikin mawuyacin hali daga makarantar sakandarin gwamnati na yan Mata dake Kawo, jihar Kaduna, sakamakon barkewar annobar kwalara inji rahoton kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daliba guda daya ta rigamu gidan gaskiya tun bayan barkewar annobar a cikin kwanakin karshen mako, kamar yadda jami’n dakile yaduwar cututtuka na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Ibrahim Suleiman ya tabbatar.

KU KARANTA: Wani dan majalisa ya sanya tukuicin N5,000,000 ga duk wanda ya yanko masa gashin Shehu Sani

Jami’in yace akalla dalibai 89 cutar ta shafa, amma zuwa yanzu an magance ta daga jikin sama da rabin daliban, sai dai ya danganta bullar cutar ga yadda daliban ke yin bayan gida a wuraren da basu dace ba, dalilin da yasa ruwan makarantar ya gurbata kenan, ya janyo wannan bala’in.

Sai dai Daraktan lafiya na jihar Kaduna, Dakta Ado Zakari wanda ya kai ziyara makarantar ya ki bayyana adadin daliban da suka kamu da cutar, amma ya shawarcesu akan hanyoyin da zasu bi wajen kauce ma kamuwa da ita.

Bugu da kari hukumar bada agajin gaggawa, Red Cross ta aika da jami’anta zuwa makarantar don wayar da musu kai akan dabarun kauce ma kamuwa da kwalara da kuma hanyoyin tabbatar da tsafta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng