Yadda Korarren Gandiroba da wata Mata suke hada baki wajen kwacewa Mutune Babura

Yadda Korarren Gandiroba da wata Mata suke hada baki wajen kwacewa Mutune Babura

- Rana dubu ta Barawo guda kuma ta mai kaya

- Asirin wasu Bariyin Babur y tonu a Minna dake jahar Minna

- Yanzu haja sun shiga hannu har ma ana haramar kai su ganin alkali

Wani korarren Ma’aikacin gidan kurkuku mai suna Abdullahi Mohammed tare da wata Mata Aisha Abubakar na daga cikin Mutane hudu da aka cafke bisa zargin kwarewa a sana’ar kwace Babura a garin mai Tumbi dake Minna ta jihar Naija.

Yadda Korarren Gandiroba da wata Mata suke hada baki wajen kwacewa Mutune Babura
Yadda Korarren Gandiroba da wata Mata suke hada baki wajen kwacewa Mutune Babura

‘Yan sanda sun bayyana cewa Abdullahi mai shekaru 30 da ita Aisha ‘yar shekara 17 tare da ragowar abokan aikata laifin nasu Abubakar Mohammed mai shekaru 30 da kuma Nasiru Aliyu shi ma mai shekaru 30 dukkanninsu mazauna unguwar PZ ne a garin Minna, suna kwace baburan Mutane ne a kauyen Shakwata.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa Barayin su kan labe ne a kauyen Shakwata, yayin da ita kuma Aisha zata zo da mai babur din da ya dauko a matsayin fasinja, nan take sai su fito daga maboyarsu su kwace masa abin hawansa, har ma zas u iya kashe shi idan yaki yarda ya ba su abinda suka nema.

Aisha ta kuma bayyana cewa Abubakar ne ya jawo ra’ayinta ta shiga cikin ayarin nasu kuma har an bata 7,000 a wani kwace da suka yi.

KU KARANTA: Taurin kai: NCS ta hana wani Jami’in da aka kora aiki da karfin tsiya kudin sa duk da umarnin Kotu

“Ni Matar aure ce, Miji na yana tsare a kurkuku bayan da aka kama shi da aikata laifi irin namu, don haka ne ma shi tsohon Gandiroban ya shawarce ni na shiga cikinsu domin hanya ce mai sauki ta samun kudi.” Aisha ta bayyana.

Mai magana da yawun ‘Yan sanda na jihar Muhammad Abubakar, ya tabbatar da faruwar kame wadanda ake zargin har ma an samu nasarar gano wasu Babura uku kirar Bajaj kuma da zarar an kammala bincike za’a gurfanar da su gaban kuliya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng