Dogo ba lamba: Mutanen da suka fi tsawo a Duniya su 12 sun shirya taro a kasar Faransa
Wai! Ni da zandoro zantorami, eh mana, wannan shine abin da zaka ji a ranka a duk lokacin da ka tsinci kanka a tsakanin mutanen da suka fi tsawo a Duniyar nan ta Ubangiji Allah, kamar yadda ya wakana a bana.
Ga duk wanda ya yi tsawon rai a rayuwa zai ga wasu abubuwa da suka saba ma hankalinsa, wanda hakan shike tabbatar da buwayar Allah madaukakin sarki, ikonsa, izzarsa, da kuma tabbatar buwayawarsa na yin duk abinda ya so.
KU KARANTA: Ruwa yayi tsami: Hukumar tsaron sirri ta janye jami’anta dake tsaron Saraki da Dogara
Legit.ng ta ruwaito an gudanar da wani taro a birnin Paris na kasar Faransa na mutanen da suka fi tsawo a Duniya, wanda ya samu halartar akalla sanannun dogayen mutane guda goma sha biyu da suka fito daga sassan kasashen Duniya.
A yayin wannan taro da ya gudana a ranar Juma’a 1 ga watan Yuni, Dogayen mutanen sun yi shawagi a dandalin Champs-Elysees dake babban birnin kasar Faransa, Paris, inda suka dauki hotuna tare da mutane a gaban gunkin Janar De-Gaulle.
Daga cikinsu akwai wani mutumi da tsawonsa ya haura mita biyu, yayinda guda daga cikinsu yake da takalmi mai lamba 68! sai dai masana ilimin halittar dan Adam sun danganta irin wannan tsawo ga wata cuta dake jikinsu.
Ga sauran hotunansu a nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng