Mutanen Zamfara su na ganin ta kan su a hannun barayin shanu

Mutanen Zamfara su na ganin ta kan su a hannun barayin shanu

- Wasu masu satar shanu sun kuma yin barna a cikin Jihar Zamfara

- An kashe mutane a wani sabon hari a Kauyen Zakuna a makon jiya

- Hakan ya zo ne jim kadan bayan an kashe mutane 20 kwanakin baya

Mun samu labari cewa duk da Sojojin da aka baza a Jihar Zamfara har yanzu ba a samu saukin kashe-kashe ba. Kwanan nan dai aka kashe mutane akalla 15 a Kauyen Zakuna da ke cikin Garin Anka.

Mutanen Zamfara su na ganin ta kan su a hannun barayin shanu
Gwamnan Zamfara tare da Shugaban Kasa Buhari da Mataimakin sa

Idan ba ku manta ba dai ba a dade da kashe mutum 26 a wani Gari cikin Muradun a cikin Jihar Zamfara. Kamar yadda mu ka samu labari an shiga Garin Zakuna ne a Ranar Juma’ar nan aka saci shanu aka kuma kashe mutane da dama.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun gayyaci Saraki ya wanke kan sa bayan ‘Yan fashi sun jefa sa cikin matsala

Mafi yawancin wadanda aka kashe ‘yansakai ne wadanda ke kokarin kare al’ummar Yankin daga ta’adin masu satar shanu da kashe Bayin Allah. ‘Yan ta’addan dai sun yi wani sabon shiri ne inda su ka fi karfin ‘Yansakan su ka kashe su kwatsam.

Rundunar ‘Yan Sanda dai yanzu su na Yankin domin kawo karshen wannan fitina inji wani babban Jami’in Jami’an tsaron. Bayan aukuwar abin ‘Yan Sandan ma dai sun ce da an sanar da su game da harin da wuri da an dauki matakin da ya dace.

Cikin dai ‘yan kwanaki kadan an rasa mutane kusan 50 a Jihar Zamfara duk da karfin Jami’an tsaron da aka baza a Yankin. Har wa yau dai kusan an rasa shawo karshen wannan matsala a Jihar Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng