An fasa gidan yarin masu aikata kisan kai a garin Minna
Wasu 'yan bindiga dadi da har yanzu ba a tabbatar da su waye ba sun kai hari wani sabon gidan yari dake garin Minna babban birnin jihar Neja, inda suka kashe mutane sannan kuma suka saki fursunoni da dama daga gidan
A cikin daren Lahadin nan ne wasu 'yan bindiga suka farwa gidan yarin bayan an idar da sallar Isha'i. 'yan bindigan sun kashe ma'aikacin gidan yarin guda tare da wani farar hula da tsautsayi ya fada ta kanshi.
DUBA WANNAN: Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka
Wani wanda aka kai harin akan shi, wanda yace bai so a ambaci sunan sa, ya bayyana cewar, gidan yarin na daure masu laifin kisa ne, saboda haka duk fursunonin da suka gudu hukuncin kisa ne a kansu.
A cikin mutane biyun da tsautsayi ya fada ta kansu daya dan acaba ne, dayan kuma ma'aikacin gidan yarin ne. A yanzu haka dai bincike ya nuna cewar fursunonin da suka rage a gidan yarin basu kai wadanda suka gudu yawa ba.
A yanzu haka dai an kawo karin jami'an tsaro gidan yarin, sannan kuma an kama wasu daga cikin wadanda suka gudu din. inji shaidar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng