Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka

Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka

- Wannan dai ba shine karo na farko da irin wannan hukunci ya faru ba a duniya, inda wasu ke kallon hakan a matsayin sanya tsattsauran ra'ayi ga addini

- Wasu gungun matasa tare da 'yan unguwa sun taru sun yiwa wata daliba jini da majina dalilin zargin ta da suke yi da aikata zina a wannan wata mai alfarma

Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka
Zargin aikata zina a watan Ramadan yasa sunyi mata dukan kawo wuka

A kasar Morocco wasu matasa mafusata kuma masu tsattsauran ra'ayi sun yima wata daliba mai kimanin shekaru 20 a duniya dan karen duka da itatuwa dalilin zargin ta da suke da aikata zina a wannan wata mai alfarma. A yanzu haka dai bidiyon lamarin ya gama zagaye kafafen sadarwa na yanar gizo, inda kowa ke tofa albarkacin bakin sa akan lamarin.

DUBA WANNAN: Anyi wani mummunan hadarin mota a jihar Jigawa

Hoton bidiyon ya nuna wasu gungun matasa masu tsattsauran ra'ayi wadanda suka hau wata yarinya da duka, wacce suke zargin kama ta a mota tare da wani tsoho.

Yarinyar tayi iya bakin kokarin ta domin ta fahimtar dasu cewar ita daliba ce, kuma tsohon da suka ganta a mota tare dashi direba ne. Sai dai matasan basu saurareta ba, nan take suka hauta da duka, inda mutanen unguwar suma suka taya su da jifan ta suna tsine mata, suna cewa "Zina a wannan wata mai albarka, amma gaskiya kinji kunya."

Lamarin yayi mutukar tayar da hankalin al'ummar duniya. inda da yawa suke ganin hakan ya wuce ka'ida, kuma kungiyoyi da yawa suke kokarin ganin an bi mata hakkin ta.

Wannan dai ba shine karo na farko da irin wannan hukunci ya faru ba a duniya, inda wasu ke kallon hakan a matsayin sanya tsattsauran ra'ayi ga addini.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng