Ruwa yayi tsami: Hukumar tsaron sirri ta janye jami’anta dake tsaron Saraki da Dogara

Ruwa yayi tsami: Hukumar tsaron sirri ta janye jami’anta dake tsaron Saraki da Dogara

Hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta kwashe rabin adadin jami’anta dake tsaron lafiyar shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar DSS ta bukaci jami’anta dake gadin Saraki da Dogara dasu garzaya babban ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja ba tare da bata lokaci ba, sai dai bata bayyana wani kwakkwarana dalilin janye su ba.

KU KARANTA: An kuma: Wasu yan Bindiga sun sake kashe Mutane 23 tare da kona gidagensu a Zamfara

Duk kokarin da majiyar ta yi na jin ta bakin hukumar DSS yaci tura sakamakon hukumar bata da wani jami’a dake magana da yawunta tun bayan nada shugabanta, Lawal Daura a shekarar 2015, sai dai jami’an majalisun dokokin Najeriya sun tabbatar da kwashe jami’an.

Ruwa yayi tsami: Hukumar tsaron sirri ta janye jami’anta dake tsaron Saraki da Dogara
Jamian DSS

Sai dai wasu rahotanni sun danganta wannan lamari ga rikicin cikin gida da ya kaure a jam’iyyar APC, inda tsagen tsohuwar PDP tawariyya da suka shiga APC ke ganin ba a musu adalci a gwamnatin APC, don haka zasu fice daga jam’iyyar.

Jiga jigan tsagen PDP Tawariyya da suka shiga APC sun hada da Sanara Bukola Saraki, Yakubu Dogara, Kwankwaso, sai kuma Atiku Abubakar da tuni yayi fatali da APC ta koma jam’iyyarsa ta asali PDP. Bugu da kari ana sa ran shuwagabannin Tawariyya zasu gana da mataimakin shugaban kasa Osinbajo a ranar Litinin, 4 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel